An kama Mutane 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani

0 112

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya tabbatar da kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan wasu mutane 12 daga Kaduna da suka yi niyyar halartar biki a jihar Filato.

Wadanda aka kashe sun fada hannun wasu matasa a yankin Mangu inda suka yi musu kwanton bauna suka kashe su ba tare da wata hujja ba.

Gwamnan ya ce ya tattauna da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang da Shugaban kasa Bola Tinubu domin tabbatar da hukunta masu laifi.

Ya kuma ziyarci wadanda suka tsira daga harin a asibitin sojoji na Kaduna tare da kira da a ci gaba da zaman lafiya.

Leave a Reply