An kama mutum biyar bisa zargin kashe ƙaramar yarinya bayan garkuwa da ita

0 201

A Najeriya, Gwamnatin jihar Kano ta ce jam’ian tsaron farin kaya na DSS sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da kisan wata ƙaramar yarinya mai suna Sakina Mamuda, a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

Mai Magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin tofa ya ce mutanen sun yi garkuwa da yarinyar ne kuma suka buƙaci biyan kuɗin fansa.

Sai dai ya ce bayan an biya su kuɗin fansar ne kuma sai kuma suka kashe ta.

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar

Leave a Reply