An kashe fararen hula da dama a yankin Tafkin Chadi na Jihar Borno

0 75

An kashe fararen Hula da dama, a yankin Tafkin Chadi na Jihar Borno, biyo bayan wani barin wuta da Sojoji suka kai kan Masu Ikirarin Jahadi a yankin Arewa Maso Gabas da kuma kasashe 3.

Wannan na zuwa ne kasa da makonni 2, bayan Sojojin sun kashe fararen hula a Jihar Yobe, biyo bayan barin wuta da suka yi musu da tunanin yan Boko Haram ne.

Majiyoyin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a kyauyen Kwantan Daban Masara dake Jihar Borno.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya rawaito cewa kimanin Masunta 20 ne Sojojin suka kashe cikin rashin sani.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya rawaito cewa wasu Mazauna Yankunan su 2, sun bayyana masa cewa kimanin Mutane 50 Sojojin Saman suka kashe a lokacin da suke Kamun kifi a tafkin Kogin.

Wata Majiya daga Rundunar Sojin Saman Najeriya ta fadawa manema labarai cewa Mutum 1 ne kawai ya rasu a lokacin harin sai kuma mutane 6 da suka samu raunika.

Kawo yanzu rundunar Sojin Najeriya bata fitar da wata sanarwa ba kan wannan batu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: