An kashe fiye da ₦2,000,000 wajen biyan hakkokin yan fansho a jihar Jigawa cikin kwanaki 100

0 254

Asusun adashen gata na fansho na jiha da kuma kananan hukumomin jihar Jigawa , yace a kwanaki dari na mulkin Mallam Umar Namadi , sun biya hakkokin maaikata fiye da naira miliyan dubu biyu.

Sakataren zartarwa na asusun Mallam Kamilu Aliyu Musa ya sanar da hakan a lokacin da yake tilawar nasarorin da asusun ya samu a kwanaki dari na Mallam Umar Namadi

Yace sun biya hakkokin maaikatan jiha da kananan hukumomi dana sashen Ilmi fiye da mutane 746

Mallam Kamilu Aliyu Musa yana mai cewar sun biya fansho na watannin Yuni da Yuli da Agusta da kuma Satumba da ya tasamma sama da naira miliyan dubu biyu da miliyan dari hudu

Yace a kwanaki dari na mulkin Mallam Umar Namadi , ya kafa kwamiti domin sake fasalin tsarin aiyukan asusun wanda hakan ya sanya kwalliya ta kara biyan kudin sabulu

Sakataren zartarwar ya kuma jinjinawa Gwamna Mallam Umar Namadi bisa kulawar da yake baiwa asusun a kowane lokaci

Leave a Reply

%d bloggers like this: