An kashe fiye da mutum 40 tare da raunata wasu 27 saboda rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya a jihar Nasarawa
An kashe akalla mutane 45 tare da raunata wasu 27 biyo bayan sabunta rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Lafia da Obi da Awe na jihar Nasarawa.
An rawaito cewa fadan farko, wanda aka fara a ranar Juma’a, ya cigaba har zuwa ranar Lahadi da dare.
Wata majiya ta ce akalla manoma dubu 5 a kauyuka 12 ne suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren da aka kai a kananan hukumomin uku.