An kashe mutane 13,346 da kuma yin garkuwa da 9,207 daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu

0 85

Tun bayan rantsar da Shugaban Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, kasar ta fuskanci ƙaruwar tashin hankali, inda aka kashe mutane dubu 13,346 da kuma yin garkuwa da dubu 9,207 a fadin kasar.

Wannan ƙaruwar rashin tsaron ta shafi ƙananan hukumomi 667 wanda yake da nasaba da ta’addanci, ƴan fashi da makami, rikicin manoma da makiyaya, da sauran rikice-rikicen zamantakewa.

Rahoton ya ce, daga watan Mayu zuwa watan Disamba 2023, an samu mace-mace 5,802 da sace mutane 2,754.

A shekarar 2024, lamarin ya ƙara tsananta, inda aka kashe mutane 7,544 aka kuma yi garkuwa da 6,453 daga watan Janairu zuwa Satumban nan.

Masana tsaro suna bayyana damuwa kan ƙalubalen tsaro da ke ci gaba da tsananta, sun kuma yi kira ga Shugaban kasar da ya ɗauki matakai masu ƙarfi don magance matsalar.

Musamman a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, domin hana shigowar ƴan ta’adda daga ƙasashen waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: