An kashe wasu jami’an soji biyu biyo bayan wata bata kashi da akayi tsakanin dakarun sojin Najeriya dana kungiyyar jami’an tsaron kudu maso gabashin kasar nan wato ESN a yankin Adani dake yankin karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar sojin kasar nan Brigadier General Onyema Nwachukwu ya rabawa manema labarai a yau laraba.

A cewar sa lamarun ya faru ne a lokacin da jami’an soji suke kokarin dakile harin da yan kungiyyar ta ESN ke kaiwa a daidai shingen Iggah zuwa Asaba dake jihar.

Haka zalika hukumar sojin ta kasa ta jaddada kudirin ta na cigaba da kare hakki da dukiyoyin al,ummar kasar nan tare da tabbatar da cewa an wadatar da tsaro a lungu da sakon kasar nan.

Haka zalika ya bukaci al’ummar yankin da su kasance masu bawa jami’an tsaro hadin kai, tare da bukatar su kasance masu kiyyaye doka da oda a fadin jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: