An kashe wasu mutane 12 a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan’uwansu

0 167

Aƙalla ƴan ɗaurin aure 12 ne aka kashe a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato a hanyarsu ta zuwa ɗaurin auren ɗan’uwansu, sannan kuma an jikkata wasu mutum 11 a lamarin wanda aka yi a ranar Juma’a.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan ɗaurin su 31 da suka taso daga garin Basawa da ke ƙaramar hukumar Zaria a jihar Kaduna, ne ciki har da mata a ƙananan yara kuma suna tafiya ne a motar bas mallakin Jami’ar ABU Zaria, kuma faɗa hannun maharan ne da misalin ƙarfe 8 na dare a hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar Qua’an Pan da ke jihar Filato.

Babban limamin masallacin Juma’a na JIBWIS, Sheikh Suleiman Haruna ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce sun ajiye gawarwakin a babban asibitin Mangu.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Ibrahim Umar ya ce, “mun je auren ɗan’uwanmu ne, sai muka ɓace hanya. Da muka tsaya domin mu yi tambaya, kawai sai suka mana ƙawanya suka fara cewa a kashe mu. Nan suka fara kashe direban, sannan suka kashe wasu, sannan suka ƙona motar. Allah ne ya tseratar da mu.”

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Filato, DSP Alfred Altau ya ce ƴansanda sun samu labarin aukuwar lamarin, kuma za su fitar da sanarwa nan gaba.

Leave a Reply