An kashe ‘yan fashin daji 10 a wasu guraren da ke fama da rikici a jihar Kaduna

0 92

An kashe ‘yan fashin daji 10 a wasu guraren da ke fama da rikici a jihar Kaduna.

Gamayyar dakarun tsaro sun yi arangama da ‘yan fashin dajin dauke da muggan makamai a Kwanan Bataru dake wajen garin Fatika a Karamar Hukumar Giwa kuma suka yi taho mu gama.

Cikin wata sanarwa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, yace daidai lokacin da ake musayar wuta, an kashe ‘yan fashin dajin su 10 yayin da wasu dayawa suka tsira da raunukan bindiga.

Ya kara da cewa ‘yan fashin dajin wadanda suka samu tserewa sun gudu sun bar babura dayawa da bingida daya da wayoyin hannu da fitulun tocilan da kuma wasu layu.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I ya yabawa dakarun tsaron bisa kashe ‘yan fashin dajin. Gwamnan ya yiwa dakarun fatan alkhairi da samun nasara a ayyukan da suke gudanarwa a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: