Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce an kusa kammala ginin wuraren harbi a manyan filayen jiragen saman kasarnan domin inganta tsaro.

Ya bayyana hakan ne jiya a Abuja yayin taron hukumar kula da filayen jiragen sama na kasa da kasa kan tsaron Afirka.

Hadi Sirika wanda Darakta-Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa, Musa Nuhu ya wakilta, ya ce ginin wuraren harbin na daya daga cikin matakan horar da jami’an tsaron jiragen sama.

Ya ce ana sa ran ginin wuraren harbin zai tsare zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa daga ayyukan katsalandan ba bisa ka’ida ba.

Hadi Sirika ya tunatar da cewa a kwanakin baya ne majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da tura karnukan tsaro zuwa tashoshin jiragen sama.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: