An kwace buhunan shinkafa 707 da wasu kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 41 da dubu 300 a jihar Jigawa

0 74

Ofishin hukumar hana fasa kwauri ta kasa Kwastan shiyyar Kano da Jigawa ya kwace buhunan shinkafa 707 da wasu kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 41 da dubu 300.

Kwanturolan ofishin, Suleiman Umar Pai, ya fada cikin wata sanarwa cewa an yi kamen tsakanin watan Yuli zuwa Satumba.

Ya kuma bayyana cewa hukumar kwastam ta kwace dila 155 ta kaya gwanjo da katan 130 na taliya da jarkokin man girki 16.

Sauran abubuwan da aka kama sun hada da katon 231 na madara da katon 8 na macaroni da kwalin maganin sauro guda 30, da katan 10 na batiri da sauransu.

Umar Pai ya kara da cewa rundunar ta tara naira miliyan dubu 16 da miliyan 900 a matsayin kudaden shiga tsakanin watan Janairu zuwa Agustan bana.

Umar Pai ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na tabbatar da ingantaccen yanayin kasuwanci mai kyau a jihoshin Kano da Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: