An kwato sama da ₦83Bn da $609M da kuma €5.4M tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023

0 100

Gwamnatin tarayya ta ce ta kwato sama da Naira biliyan 83 da dala miliyan 609 da kuma Yuro miliyan 5.4  tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023 lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Har ila yau, ta bayyana cewa an ajiye duk kudaden da aka kwato a cikin asusun ajiyar kadarorin FGN wanda ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) ke kula da shi a babban bankin kasa (CBN).

Daraktan shirin shugaban kasa kan ci gaba da binciken kudi (PICA), ma’aikatar kudi, Yusuf Sule, ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a Abuja, a wani taron wayar da kan jama’a kan, “Aiwatar da manufofin boye bayanan sirri , Batutuwa, kalubale da kuma hanyoyin ci gaba.”

Duk da irin kalubalen da ake fuskanta, Sule, wanda ya gabatar da rahoton halin da ake ciki game da aiwatar da manufofin ya bayyana cewa an samu wasu muhimman abubuwa. Ya bayyana cewa an bullo da wannan manufar ne domin karfafa wa ‘yan kasa gwiwa wajen yakar cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: