An lalata allurar cutar Corona ta AstraZeneca kimanin Miliyan 1 da dubu 66 da 240

0 66

Hukumar Lura da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) tare da Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Kasa sun Lalata Rigakafin Cutar Corona ta AstraZeneca kimanin Miliyan 1 da dubu 66 da 240.

Kimanin rigakafin Miliyan 1 da dubu 527 da Dari 886 aka yiwa Jama’a daga cikin Alluran da aka kawo su kasar nan kafin su lalace.

Rigakafin da aka lalata a yau wa’adin su ya kare ne tun cikin watan Nuwamba.

An lalata Alluran ne a yankin zuba shara na Gosa wanda ya ke da nisan Kilomita 2 tsakanin sa da Tashar Jirgin Kasa na Idu dake Abuja.

Shugaban Hukumar Lura da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce amincewa da lalata rigakafin ya biyo bayan karewar wa’adin su.

Haka kuma ta ce hakan ya zama dole domin kare lafiyar yan Najeriya ba tare da cutar dasu ba.

A jawabinsa, Sakataren Zartarwa na Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Kasa Dr Faisal Shu’aib, ya ce rigakafin da aka kawo suna da wa’adin Makonni 2 kafin su lalace a lokacin da aka kawo su.

Dr Faisal, ya ce kawo yanzu mutane Miliyan 10 ne kacal aka yiwa rigakafin cutar ta Corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: