An lalata kayayyakin abinci da aka yiwa algus na sama da Naira miliyan 6 a Jigawa

0 68

Kwamitin Kare Hakkin Mai Saye na Jihar Jigawa ya ce ya lalata kayayyakin da aka yiwa algus na sama da Naira miliyan 6.

Shugaban kwamitin, Alhaji Farouk Abdallah Malam Madori ya bayyana hakan jiya ga manema labarai a ofishinsa.

Ya ce kwamitin ya yi nasarar lalata kayayyakin abinci da aka yiwa algus, da sauran kayayyaki na miliyoyin nairori daga shekarar 2015 zuwa yau.

Faruk Malam-Madori ya bayyana wasu daga cikin kayayyakin da suka hada da gero, masara, wake, ridi da zobo, wadanda duk an gurbata su kuma an kai su kasuwanni daban-daban a fadin jihar.

Ya ce daya daga cikin ayyukan kwamitin shi ne tabbatar da cewa jihar ta aminta daga duk wasu nau’ikan kayayyakin abincin da aka gurbata da magunguna.

Farouk Abdallah ya ce kotun tafi-da-gidanka ta kwamitin ta karbi tarar sama da naira miliyan 4.

Leave a Reply

%d bloggers like this: