An lalata matatun danyen mai 25 a jihohin Imo da Ribas

0 107

Hare-haren da dakarun sojin saman, suka kaddamar sun kashe gomman ‘yan bindiga a jihohin Kaduna da Zamfara, tare da lalata matatun danyen mai 25 a jihohin Imo da Ribas.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Edward Gabkwet ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Ya ce rundunar ta Operation Whirl Punch ta ci gaba da aikinta na gano sansanin ‘yan bindiga tare da kawo karshensu.

Ya ce bayanan sirrin sun nuna cewa ‘yan bindigar da ke addabar al’umma a karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja suna zaune ne a Jihar Kaduna.

A cewarsa, karin bayanan sirri sun nuna cewa wadannan ‘yan bindigar suna yin balaguro daga dajin Allawa na Jihar Neja zuwa dajin Malum na karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: