Gwamnatin tarayya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta (UAE) sun yi nasarar cimma yarjejeniyar barin masu riƙe da fasfo na Najeriya su koma yin tafiye-tafiye zuwa ƙasar ta UAE.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya ba da sanarwar yarjejeniyar. Ya bayyana cewa za a fara maido da bai wa ‘yan Nijeriya bizar zuwa UAE daga ranar 15 ga Yuli, 2024, tare da sababbin sharuɗɗan samun bizar.
‘Yan Nijeriya da ke son duk wani ƙarin bayani game da sharuɗɗan bizar da UAE ta sabunta za su iya ziyartar yanar gizon gidan.