Wata kungiyar farar hula mai suna Zamfara Circle, ta maka kamfanonin sadarwar wayar salula kara a gaban kotu tana neman a biya su diyyar naira miliyan 100 saboda rufe hanyoyin sadarwar wayar salula a jihar.
Kamfanonin MTN, Glo, 9mobile da kuma Airtel sune wadanda ake tuhuma a karar.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, kwamishinan shari’a da kuma babban lauyan jihar da kuma hukumar sadarwa ta kasa (NCC) suna daga cikin wadanda ake tuhuma a karar.
Gwamna Matawalle ya bayar da umarnin dakatar da hanyoyin sadarwar wayar salula a jihar a wani mataki na magance matsalar rashin tsaro.
An dawo da hanyoyin sadarwar a wasu sassan jihar bayan an duba yanayin tsaro amma har yanzu kananan hukumomi shida ba su da hanyoyin sadarwar wayar hannu.
A karar da aka shigar a wata kotu da ke Gusau babban birnin jihar, kungiyar ta Zamfara Circle, ta ce rufe hanyoyin sadarwar ya jawo wahalhalu da asara ga masu amfani da wayoyin hannun.