An maka wani lauya a kotu da aka kama da sayar da fili sau biyu a jihar Yobe

0 84

Wani dan kasuwa, Alhaji Baka Abdu, ya maka Lauya, Bala Dala, a gaban wata Babbar Kotu da ke Potiskum a jihar Yobe, bisa sayar da fili sau biyu, wanda aka sayar akan naira miliyan 110.

Lauyan wanda ya shigar da kara, Barista Isaac Ambule, ya roki kotu da ta soke cinikin filin da Bala Dala ya siyar wa Sanata Ibrahim Bomoi.

Ya bayar da hujjar cewa an siyar da filin ga wanda yake karewa da farko, wanda ya biya kudin amma daga baya ya gano cewa an sake sayar da wannan fili ga Sanatan.

Sai dai lauyan wanda ake kara, Hakeem Akilola, ya musanta ikirarin mai karar sannan ya roki kotu da ta yi watsi da karar saboda rashin cancanta.

Ya kara da cewa wanda yake karewa ya bi hanyar doka a cinikin da ake takaddama akai.

Bayan sauraron bangarorin biyu, alkalin kotun, Mohammed Zannah, ya dage karar zuwa ranar 4 ga Oktoba, 2021, don ci gaba da sauraron karar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: