Hukumar gudanarwar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta naɗa Farfesa Adamu Ahmed a matsayin sabon shugaban Jami’ar.
Shugaban hukumar, Mahmud Yayale Ahmad ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke jagorantar taron hukumar karo na 209 a yau Laraba.
Kafin naɗin nasa, sabon shugaban Jami’ar Farfesa Adamu, malami ne a sashen karatun tsara birane a jami’ar, kuma zai maye gurbin tsohon shugaban jami’ar Farfesa Kabir Bala.
– BBC Hausa