An raba sama da naira miliyan 768 da dubu 900 ga maniyyatan da suka nemi a biya su kudadensu a jihar

0 72

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina ya zuwa yanzu ta raba sama da naira miliyan 768 da dubu 900 ga maniyyata 599 da suka nemi a biya su kudadensu a jihar.

Daraktan zartarwa na hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ne ya bayar da wannan bayanin yayin ganawa da manema labarai kan aikin mayarwa da maniyyata kudadensu na haji na shekarar 2020 da 2021 a helkwatar hukumar da ke Katsina.

Suleiman Kuki ya ce adadin shine kashi 22.01 na jimillar maniyyata dubu 2 da 721 da suka ajiye kudadensu ga hukumar.

Ya ce, duk da haka aikin na ci gaba da gudana kuma duk wani maniyyaci da ke da niyyar neman a mayar masa da kudin ajiyarsa, zai iya bukatar hakan.

Daraktan ya jaddada cewa, wadanda ke son jujjuya kudaden su kafin aikin hajjin badi, suma zasu iya yin hakan ta hanyar tuntubar ofisoshin maniyyatan su na shiyya don mika bukatarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: