An sallami wasu sojoji daga aiki bisa yin wata gagarumar sata a matatar manfetur ta Dangote

0 236

An sallami wasu sojoji da aiki bisa yin wata gagarumar sata da suka yi a matatar manfetur ta Dangote

Rundunar sojin Najeriya, a ranar Litinin, ta ce ta kori sojoji biyu, wadda ya hada da Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani, da ake zargi da satar wasu igiyoyin waya masu muhimmanci a matatar man fetur ta Dangote a ranar 14 ga Afrilu, 2024.

Gidan jaridar PUNCH ya ruwaito yadda sojojin suka shiga cikin matatar a cikin wata mota kirar Acura jeep amma an cafke su a babbar kofar kamfanin da wayoyin keburan har guda 897.

Leave a Reply

%d bloggers like this: