Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta ce ta samu barkewar gobara sau 114 da kuma mutuwar mutane shida a watan Janairu a wasu yankuna uku na jihar.

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Paul Aboi ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa yau a Kaduna.

Ya ce gobarar ne daban-daban a biranen Kaduna, Zariya da Kafanchan.

Paul Aboi ya ce hukumar ta ceto mutane 4 ba tare da sun samun rauni ba, yayin da takwas suka samu raunuka sakamakon wutar.

Paul Aboi ya ce rashin kulawa da amfani da na’urorin wutar lantarki ta hanyar da bata dace ke haddasa tashin wuta, inda ya bukaci mazauna yankunan da su dauki matakan kariya domin kaucewa afkuwar gobara.

Daraktan ya ce hukumar na yin iya bakin kokarinta wajen ganin an rage barkewar gobara ta hanyar wayar da kan jama’a kan matakan kariya daga gobara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: