An shawaci Tinubu da ya samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasa

0 147

Wasu fitattun masu rajin kishin ƙasa daga sassa daban-daban, ƙarkashin jagorancin tsohon babban sakataren ƙungiyar ƙasashe renon Ingila (Commonwealth), Cif Emeka Anyaoku, sun shawarci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya ɗauki matakin samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.
Tawagar mutanen ta gabatar da buƙatar hakan ne, a lokacin da ta ziyarci Shugaban a Abuja, inda ta ba shi shawarwari da dama game da gaggan matsalolin da suka dabaibaye kasar.
Ya ce tawagar tasu na ganin bai kamata a ce Najeriya tana da majalisun dokoki na tarayya biyu ba, wato ta dattawa da kuma ta wakilai, kamata ya yi a ce guda ɗaya ce.
Sannan ya ce akwai buƙatar samar da ma’aikatun tsaro na yankuna, domin hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da ake fama da ita.
Tsohon sanatan ya ce, suna ganin muddin ba a samar da sabon kundin tsarin mulki ga najeriyar ba to haka za a yi ta tafiya a ƙasar.
Ya ce shugaban kasar ya yi alƙawarin duba shawarwarin da suka ba shi, tare da gayyatar jagoran tafiyar Chief Emeka Anyaoku nan gaba kadan kan batutuwan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: