An shawarci daliban Arewacin Kasarnan da ke manyan makarantun kasarnan da su tashi tsaye a zaben 2023 domin maye gurbin duk shugabanin da ba nagari ba, a dukkanin matakai wadanda suka lalata kasarnan cikin shekaru 20 da suka gabata.

Shugaban kwamitin lakcocin shugabanci na Maitama Sule, Alhaji Shehu Dalhatu ne ya bayar da wannan nasihar a jiya a wajen wani taron da reshen dalibai na gamayyar hadin kan kungiyoyin Arewa ta shirya a kwalejin ilimi dake Gumel a jihar Jigawa.

A cewar Shehu Dalhatu, galibin wadanda ke rike da mukaman shugabanci a kananan hukumomi da majalisun jihohi ‘yan kasa da shekaru 40 ne, kuma ya yi mamakin dalilin da ya sa dalibai masu shekaru daya basa taka musu birki idan suka kauce hanya, tare da tabbatar da yin abin da ya dace domin cigaban kasarnan.

A jawabin da ya gabatar, Dr Saidu Ahmed Dukawa, wani malamin jami’a, ya lura cewa, domin nuna muhimmancin sa ido kan al’amuran da suka shafi al’ummar kasarnan, alkaluma sun nuna cewa an samu karuwar daliban da ake dauka, daga dubu 2 a shekarar 1900 zuwa sama da miliyan biyu a shekarar 2020.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: