An Shiga Tashin Hankali da Shugaban Ƙaramar Hukuma Ya Sume ana tsaka da Taron APC

0 449

Magoya bayan APC sun shiga firgici da tashin hankali da shugaban karamar hukumar Bariga ta jihar Legas, Kolade Alabi ya sume a wurin taron Kolade, wanda shi ne shugaban kungiyar shugabannin ƙananan hukumomi (ALGON) ya yanke jiki ya faɗi a taron masu ruwa da tsakin APC a Legas An ruwaito cewa likitoci da hadimansa sun yi ƙoƙarin dawo da shi hayyacinsa kafin daga bisani aka garzaya da shi asibiti mafi kusa.

An shiga wani hali na firgici da rudani a ranar Laraba da rana, yayin wani taron masu ruwa da tsakin APC da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke titin Acme, jihar Legas. Mahalarta taron sun shiga yanayin tashin hankali lokacin da shugaban ƙaramar hukumar Bariga, Alhaji Kolade David Alabi ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taron.

Leave a Reply