An shigar da shugaban kasa Muhammadu Buhari kara a gaban kotu saboda son daukar bayanan yan Najeriya ta WhatsApp

0 139

Kungiyar SERAP mai fafutukar kare hakkin bil’adama a kasarnan ta shigar da shugaban kasa Muhammadu Buhari kara a gaban kotu tana neman kotun ta haramta shirin gwamnati na bibiya da kutse da sanya ido kan sakonnin whatsapp da kiran waya da sakonnin karta kwana na ‘yan Najeriya da sauran mutane, lamarin da ta kira ya take hakkin ‘yan Najeriya na sirrikansu.

Shigar karar ya biyo bayan kwarya-kwaryar kasafin kudin da aka sanyawa hannu a watan Yulin bana na kashe kudi naira Miliyan dubu 4 da Miliyan 870 wajen sanya ido akan kiraye-kirayen waya da sakonni.

Adadin kudin bangare ne na kudi naira Miliyan dubu 895 da Miliyan 800 na kwarya-kwaryar kasafin kudi wanda majalisar kasa ta amince da shi.

An shigar da karar a ranar Juma’ar da ta gabata a gaban babbar kotun tarayya.

Daga cikin wadanda aka shigar da karar tare da su akwai ministan shari’ah kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, da ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed.

Leave a Reply

%d bloggers like this: