An tabbatar da Pantami a matsayin Farfesa

0 93

Kwamitin binciken kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ya wanke hukumomin jami’ar fasaha ta tarayya da ke Owerri (FUTO) daga cece-kucen da ake yi na nadin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, a matsayin Farfesa na Tsaron Intanet.

Jami’ar ta ce, ta bi ka’idojin da suka dace kuma ta gabatar da wallafe-wallafen Pantami don tantancewa ga masu tantancewa na waje, sannan kuma ta kafa ka’idar farko don nada shi Farfesa na Tsaron Intanet.

Kwafin rahoton mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa MS Nwakaudu da wasu mambobi hudu ya bayyana irin matakan da jami’ar ta bi wajen nada Pantami a matsayin Farfesa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: