An tsamo gawar mutane aƙalla 141 da kwale-kwale ya kife da su a jihar Neja

0 150

Hukumomi a Najeriya sun ce sun tsamo aƙalla gawarwaki 141 daga cikin mutanen da kwale-kwale ya kife da su ranar Talata a kogin Neja.

Kawo yanzu akwai ragowar mutum 52 da ba a gani ba, waɗanda ake fargabar cewa sun mutu.

Kwale-kwale ta tashi ne daga ƙauyen Gwajibo Mudi, na ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara ɗauke da fasinjoji aƙalla 300 da ke kan hanyarsu ta zuwa maulidi a garin Gwajibo na jihar Neja mai maƙwabtaka.

Jirgin ya kife ne da fasinjoji fiye da 150 galibinsu mata da ƙananan yara, lamarin da ya jefa al’ummar yankin da dama cikin mawuyacin hali da fargaba.

Tuni dai shugaban Najeriya Bol Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbain hatsarin.

Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarni ga jami’ai su tabbatar masu tuƙa kwale-kwalen ba su saɓa dokar haramcin tafiye-tafiye cikin dare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: