An tsinci gawarwakin mutane 2 mace da namiji a cikin wata mota a karamar hukumar Fagge ta cikin Kano

0 130

An tsinci gawarwakin mutane 2 Mace da Namiji a cikin wata Mota a karamar hukumar Fagge ta cikin Kano kan hanyar Katsina a jiya Juma’a.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana sunan mutanen a matsayin Steven Ayika wanda yana da aure da yaya 2, sai kuma Chiamaka Emmanuel, wanda zata yi aure a watan Disamba.

Wani shaidar gani da ido ya ce an ajiye motar ne a gefen titi kuma motar tana da bakin gilashi.

Shaidar ya ce an gano cewa an rufe gilashin motar, tare da kashe wayoyin su.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar bincike na musamman, sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, kuma sun garzaya da mutanen zuwa Asibiti inda aka tabbatar da mutuwar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: