An ware kudi naira miliyan dubu 25 domin tallafawa ‘yan kasuwa a Jihar Jigawa

0 138

Cibiyar ‘Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adinai da Aikin Gona ta kasa reshen jihar Jigawa tace an ware kudi naira miliyan dubu 25 domin tallafawa ‘yan kasuwa wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Shugaban cibiyar Muktari Muhammad Birniwa ya sanar da hakan ta wani shirin Radio Jigawa.

Yace majalissar aikewa da kayayyaki zuwa kasashen waje ta kasa da hadin gwiwar cibiyar sun gudanar da taron bita ga manoman jihar Jigawa kan hanyoyin aikewa da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Ya kara da cewa a yanzu haka mutane 19 ‘yan jihar Jigawa sun sami tallafin kudade da ya kama daga naira miliyan 4 zuwa fiye da naira miliyan 10.

Muktari Birniwa ya bukaci manoma da ‘yan kasuwa da su tabbatar sun yi rijista da hukumar yiwa kamfanoni rijista ta kasa domin amfana da tsare-tsaren gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: