An yanke wa tsohuwar Shugabar Myanmar hukuncin shekara huɗu a gidan yari

0 168

An yanke wa tsohuwar Shugabar Myanmar, Aung San Suu Kyi, hukuncin shekara huɗu a gidan yari wanda shi ne hukuncin farko a shari’ar da za a iya yanke mata hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

An same ta da laifin haddasa tarzoma da karya dokar yaƙi da korona.

Ms Suu Kyi na fuskantar tuhuma 11, waɗanda ake kallo a matsayin na rashin adalci. Sai dai ta musanta zarge-zargen.

Ta shafe lokaci mai tsawo a ɗaurin talala tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabarairu, inda suka hamɓarar da gwamnatinta.

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan ko za a kai ta gidan yarin ko kuma yaushe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: