An yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe wata mata da fartanya a Gumel

0 58

Babbar Kotun Jihar Jigawa da ke zama a Gumel a jiya ta yanke wa wani Habibu Haruna hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe wata mata da fartanya.

Alkali mai shari’a, M.A Sambo ya ce kotun ta samu Habibu Haruna na Kauyen Dan Makama da ke karamar hukumar Sule Tankarkar da laifin kisan kai.

Ya ce lauyan masu gabatar da kara ya gabatar da shaidu biyu tare da gabatar da bayanai, kuma wanda ake tuhuma ya bayar da shaida don kare kansa.

Sambo ya ce rahoton likita ya tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ya yi amfani da fartanya da sanda ya buga wa Aisha Adamu a goshi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar ta.

Ya ce laifin yana da hukuncin kisa a karkashin sashi na 221 na kudin manyan laifuka.

Bayan gamsuwa da bayanin masu gabatar da kara, kotun ta samu Haruna da laifin kisan kai, don haka ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: