An yi fatali da ƙarar da aka ɗaukaka kan zaɓen gwamnan jihar Benue

0 291

Kotun ƙoli ta yi fatali da ƙarar da aka ɗaukaka kan zaɓen gwamna Hycinth Alia na jihar Benue.

Matakin na zuwa ne bayan janye ƙarar da lauyan Mr Titus Uba na Jam’iyyar PDP, Sebastian Hon ya yi.

Titus Uba ya ƙalubalanci nasarar gwamna Hyacinth ne na jam’iyyar APC.

Sai dai kotun ƙararrakin zabe da ta ɗaukaka ƙara a Abuja sun tabbatar Alia ne halastaccen gwamnan jihar ta Benue bayan da hukumar aɓe INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

PDP da dantakarar ta na zargin mataimakin gwamnan jihar da mallakar takardar boge.

A wani labarin kuma, Kotun ƙolin ta ce nan gaba ne za ta sanar da za ta yanke hukunci kan karar da aka ɗaukaka kan zaɓen gwamna na jihar Ebonyi.

Alƙali John Okoro ya ɗauki matakin ne bayan da ɓangarorin da ke shari’ar suka amince da jawaban da suka yi gaban kotun. Kotun ɗaukaka ƙara a jihar Legas tun farko ta tabbatar da Francis Nwifuru a matsayin halastaccen gwamnan jihar Ebonyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: