An yi nasarar kashe wani da ake zargin kasurgumin dan bindiga ne a jihar Katsina

0 89

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa karkashin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tare da hadin gwiwar sojoji, da jami’an Civil Defence, da kuma ‘yan banga sun yi nasarar kashe wani da ake zargin kasurgumin dan bindiga ne tare da cafke wasu mutane biyu.

Aikin sintirin da aka gudanar a kananan hukumomin Dandume da Sabuwa na jihar, ya yi sanadiyyar kwato baburan ‘yan bindiga guda biyu a kauyen Madachi da ke karamar hukumar Sabuwa.

An samu wannan nasarar ne bayan da tawagar tayi musayar wuta da wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne a ranar Juma’a a yayin da suke wani samame. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, ya ce rundunar ta samu nasarar dakile harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: