An yiwa ƙanana yara 55,037 rigakafin shan-inna a ƙaramar hukumar Guri da ke jihar Jigawa

0 115

A ƙaramar hukumar Guri da ke jihar Jigawa, an samu nasarar yiwa yara ƙanana guda 55,037 masu ƙasa da shekara biyar rigakafin shan-inna a watan Yuni karkashin shirin rigakafin da aka kammala kwanan nan. 

Manajan hukumar kula da lafiyar matakin farko a yankin, Hassan Hassan Yayari, ne ya bayyana hakan ga jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Fahad Mallam Madori, jim kaɗan bayan tabbatar da sakamakon aikin rigakafin na tsawon kwanaki biyar. 

Yayari ya yaba da cikakken goyon bayan shugaban ƙaramar hukumar, Hon Abubakar Umar Danbarde, tare da nuna godiya ga iyaye da shugabannin gargajiya bisa yadda suka rungumi rigakafin da nufin kawar da ragowar cutar shan inna daga yankin.

A nasa jawabin, Hon Danbarde ya sake jaddada kudirin majalisar sa na ci gaba da bayar da tallafin kuɗi da na kayan aiki a duk wani zagaye na rigakafi.

Leave a Reply