An yyana karin kananan hukumomi 4 na jihar Jigawa a matsayin wadanda suka fice daga cikin Kananan hukumomin da ake Bahaya a bainar jama’a

0 88

Ma’aikatar Albarkatun ruwa ta Kasa ta ayyana karin Kananan Hukumomi 4 na Jihar Jigawa a matsayin wadanda suka fice daga cikin Kananan hukumomin da ake Bahaya a bainar Jama’a, kamar yadda hakan yake cikin kudurin shekarar 2017.

Kananan Hukumomin sune Hadejia, Ringim, Malam Madori da kuma Kiri Kasamma.

Ma’aikatar ta ce hakan ya kawo adadin yawan Kananan hukumomin da suka fita daga cikin matsalar zuwa 71 daga cikin 774 da suke Kasar nan.

A taron Bidiyon kai tsaye da Kwamatin Yaki da Matsalar ya gudanar karkashin Jagorancin Mista Emmanuel Awe, ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa kafin Kananan Hukumomi su fita daga cikin matsalar, dole ne a kauracewa yin bahaya a bainar Jama’a da kuma tsaftar muhalli da ta Jiki.

Kazalika, ya bukaci sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an cigaba da tsaftace muhallan su domin cigaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: