An zaɓi Cardinal Prevost a matsayin sabon Fafaroma

0 80

Robert Francis Prevost ya zama Fafaroma na farko ɗan asalin ƙasar Amurka a wannan Alhamis, inda yanzu za a riƙa kiransa, Fafaroma Leo na 14, bayan da manyan fadodin majami’ar Katolika da ake kira  Cardinals suka zabe shi don ya jagoranci mabiya biliyan 1 da miliyan 400.

An haifi sabon Fafaroman ne a ranar 14 ga watan Satumban shekarar 1955 a birnin Chicago na jihar Illinois, ta Amurka ga iyalin Louis Marius Prevost, mai asali da Faransa da Italiya, a yayin da mahaifiyarsa, Mildred Martínez ‘yar asalin Spain ce.

Ya shafe ilahirin yarantarsa tare da iyayensa, inda  ya fara karatu a ƙaramar makarantar koyon addini ta mabiya aƙidar Agustine ta Katolika, wato  Augustinian Fathers, bayan nan ya  garzaya jami’ar  Pennsylvania, a shekarar 1977, inda ya samu digiri a lissafi da falsafa.

A birnin Rome na Italiya aka naɗa shi a matsayin limamin Katolika a ranar 19 ga watan Yunin shekarar 1982, bayan ya ƙaro ilimin addini.

Fafaroma Leo na XIV, shine shugaban Kiristoci mabiya mazahabar Katolika na biyu da ya fito daga nahiyar Amurka, bayan Fafaroma Francis wanda dan ƙasar Argentina ta Kudancin Amurka ne, sai dai wannan sabon Fafaroman, ɗan ƙasar Amurka ne a Arewacin nahiyar.

Ya samu ilimin addinin mai zurfi a makarantar Catholic Theological a jihar Chicago ta Amurka. Yan ɗan shekara 27 aka tura shi birnin Rome don ya karanci dokokin addini na Canon Law a jami’ar  Saint Thomas Aquinas.. 

Sabon Fafaroman, wato Cardinal Robert Francis Prevost,maiinkiya da Leo na 14, shine shugaban mabiya ɗarikar Katolika na 267, kuma wanda ya gaji marigayi Fafaroma Francis, wanda ya rasu a  watan da ya gabata.

Leave a Reply