An zaɓi wanda yayi zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a matsayin shugaban ƙasar Chile

0 321

An zabi dan majalisa mai sausaucin ra’ayi wanda yayi farinjini lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar Chile, a matsayin shugaban kasar na gaba.

Da kimanin kashi 99 cikin 100 na sakamakon zaben da aka sanar a rumfunan zabe, Gabriel Boric ya lashe kashi 56 cikin 100 na kuri’un da aka kada, idan aka kwatanta da kashi 44 cikin 100 na abokin karawarsa, Jose Antonio Kast, mai tsatstsauran ra’ayi.

A wani lamari da ya nuna kyakykyawar dangantaka bayan gangamin yakin neman zabe, Antonio Kast ya gaggauta amincewa da shan kaye, inda ya wallafa wani hotonsa yana waya tare da abokin karawarsa yana taya shi murna.

Dan shekara 35, Gabriel Boric yana shirin zama shugaban kasar Chile mafi karancin shekaru a tarihin kasar.

Shugaban kasa mai barin gado, Sebastian Pinera, ya shirya tattaunawa ta internet tare da Gabriel Boric yana mai tabbatar masa da cikakken goyon bayan gwamnati a watanni uku na shirin mika mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: