Ana ci gaba da jin karar harbe-harbe a birnin Khartoum na kasar Sudan duk da matsin lambar da ake yiwa kungiyoyin da ke gaba da juna na su tsagaita wuta.
Wata mai fafutukar tabbatar da adalci da dimokuradiyya a birnin Khartoum, Hala Y Alkarib, ta shaida wa manema labarai cewa har yanzu tana jin karar manyan bindigogi a kusa da ita.
Rahotanni sun ce sojojin Sudan da wata kungiyar sa-kai da ake kira RSF suna ci gaba da gwabza kazamin fada domin kwace iko da hedkwatar sojojin da ke babban birnin kasar.
Tashar talabijin ta Al-Arabiya ta bayar da rahoton karar tashin bama-bamai da manyan bindigogi a kewayen hedkwatar a yau.
An kuma bayar da rahoton gwabza fada a kusa da filin jiragen sama na Khartoum da wasu wurare a biranen Omdurman da Khartoum Bahri.
Bangarorin biyu dai sun yi ikirarin iko da rundunar sojin kasar da kuma babban filin jirgin sama.
Kasashen duniya da dama sun yi ta kiraye-kirayen a kawo karshen fadan da ake yi, wanda yanzu ya shiga rana ta hudu kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 200.