Dakarun yankin Gabashin Afirka sun cika wata guda tun bayan fara yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ‘yan tawayen M23.
Kakakin ‘yan tawayen Willy Ngoma ya shaidawa manema labarai cewa mayakan na M23 na zuwa yankunan da aka ware domin wanzar da zaman lafiya.
Sai dai ana ci gaba da nuna damuwa kan ko zaman lafiya zai dore a gabashin kasar.
M23 ta dage cewa ba za ta kwance damarar makamai ba, sai dai idan gwamnati ta amince da tattaunawa kai tsaye, lamarin da shugaba Félix Tshisekedi ya yi watsi da shi.
A farkon shekarar da ta gabata ne kungiyar ta M23 ta fara hada kan yayanta, shekaru goma bayan kwance damara a matsayin wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya, tare da fara kwace yankuna a lardin North-Kivu.
Dubban daruruwan fararen hula da suka tsere daga gidajensu na ci gaba da zama a sansanoni saboda fargabar komawarsu har sai an tabbatar da tsaronsu.
- Comments
- Facebook Comments