Ana cigaba da bayyana mutanen da suka rayukansu a harin da yan bindiga suka kaiwa jirgin kasa a hanayar Abuja zuwa Kaduna

0 125

Daya daga cikin wadanda suka shaida harin da aka kai kan jirgin kasa jiya da dare sun ce ‘yan fashin dajin sun yi musayar wuta da sojoji na tsawon kimanin awanni 2.

Wanda ya shaida lamarin da baya so a fadi sunansa, yace an kashe mutane shida, ciki har da masu sayar da abinci, yayin harin.

Maharan sun yi amfani da abubuwan fashewa wajen lalata digar jirgin, lamarin da ya sanya jirgin ya tsaya kuma suka samu shiga ciki.

An rawaito cewa an dauki wadanda suka raunata da gawar wadanda suka rasu zuwa asibitin sojoji na 44 dake Kaduna. Kuma gwamnati ta umarci dukkan asibitoci su yiwa wadanda suka jikkata magani a kyauta, tare da alkawarin biyan kudin.

A wani batun kuma, hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta kasa ta dakatar da zirga-zirga akan hanyar jirgin kasa ta Abuja zuwa Kaduna, biyo baya harin ‘yan ta’adda.

Hukumar ta tabbatar da matakin cikin wata sanarwa da ta fitar yau ta shafinta na Twitter.

Leave a Reply

%d bloggers like this: