Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce ana matsa masa lamba sosai kan ya bayyana wanda zai gaje shi kafin zaɓen 2027.
Ya bayyana haka ne a wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar a Keffi, inda ya ce zai sanar da wanda yake so a lokacin da ya dace.
Wasu na ƙoƙarin ganin cewa mulki ya koma yankin Nasarawa ta yamma, amma wasu sun gargadi gwamnan da kada ya zabi wanda ba ya da karɓuwa.
Ya tabbatar cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci.