Ana Tsare Da Fursunoni Sama Da 52,446 Masu Zaman Jiran Shari’a A Gidajen Yarin Dake Fadin Kasarnan

0 79

Hukumar da ke kula da gidajen gyaran da’a ta kasa ta ce fursunoni sama da dubu 52 da 446 da ke zaman jiran shari’a sun yi yawa a gidajen yarin da ake tsare da su a fadin kasarnan.

Mataimakin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran da’a ta kasa, Gimba Dumbulwa ne ya bayyana hakan yayin wani babban taro kan rage cunkoso da aka gudanar jiya a Abuja.

Gimba Dumbulwa ya ce wasu daga cikin fursunonin sun kasance a daure tsawon sama da shekaru 10 ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

Ya ce cunkoson gidajen yari na ci gaba da zama babbar matsala wajen kula da fursunonin a kasarnan.

Gimba Dumbulwa ya ce kokarin da babban kwamandan hukumar kula da gidajen gyaran da’a Haliru Nababa ya yi na ganin an rage cunkoso a gidajen yarin ya biyo bayan tsaikon da ake samu wajen shari’ar fursunonin.

Ya ce hanya daya tilo da hukumar kula da gidajen gyaran da’a za ta dauka ita ce ta mayar da fursunoni daga gidajen yari masu cunkoso zuwa wasu da babu cunkosu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: