Ofishin Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa na Jihar Jigawa ya nuna damuwar cewa wasu mazauna kauyukan da ke kan iyakokin kasarnan a jihar Jigawa suna ba yar da mafaka ga wadanda ake zargin masu fataucin mutane ne a kan iyakokin Jamhuriyar Nijar.

Kwanturolan hukumar shige da fice a jihar, Ismail Abba Aliyu, ya yi wannan gargadin yayin da yake yi wa manema labarai bayani game da kubutar da wasu ‘yan mata hudu da ake zargi daga hannun wadanda ake zargin masu fataucin mutane ne.

Ya ce an kubutar da su ne a ranar Alhamis a kauyen Gurin, kan hanyar Babura daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar a kan hanyarsu ta zuwa Tripoli, babban birnin kasar Libya.

Ya ce rundunar Operation Salama dake kula da yankin Kazaure, Babura da Ringim na jihar ne ta samu nasarar wannan kamen.

Abba Aliyu ya ce wadanda ake zargin wadanda dukkansu mata ne, sun fito ne daga yankin kudancin kasar, ya kara da cewa wasu mutane 26 da direban motar da ke dauke da ‘yan matan sun tsere.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: