Angudanar da ayyukan noma na fiye Naira miliyan 17,000 a kananan hukumomin 5 na jihar Jigawa

0 65

Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar bankin cigaban Afrika sun gudanar da ayyukan noma da kudinsu ya kai naira miliyan dubu 17 da miliyan 700 a kananan hukumomin 5 na jihar Jigawa.

Sanata mai wakiltar Jigawa ta arewa maso gabas Barista Ibrahim Hassan Hadejia ya sanar da hakan a lokacin duba wasu daga cikin ayyukan a kananan hukumomin Auyo da kuma Kafin Hausa

Yace an gudanar da ayyukan ne karkashin shirin bayar da tallafin farfado da aikin gona na gwamnatin tarayya.

Ibrahim Hassan ya kuma yabawa Gwamna Badaru Abubakar bisa hadin kai da goyan baya da ya bayar wajen samun saukin aiwatar da shirin.

A jawabinsa babban jamiin kula da shirin, Auwalu Ado Shehu, ya jinjinawa gwamna Badaru Abubakar bisa yadda yake biyan kudaden shirin akan lokaci.

Yace ayyukan da aka gudanar sun cimma kashi 50 cikin 100 na kammaluwa kuma sun hada da hanyar birji daga Hadejia Jamaare zuwa Ansaye zuwa Galauchi zuwa Miga da kuma ta Auyo zuwa Zabarau zuwa Gudito ta wuce zuwa Maskangayu domin kai kayan abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: