Masu garkuwa da mutane sun sace mutum sama da dari (100) a cikin kauyen Shadadi dake karamar hukumar Mariga dake Jihar Niger.

Mazauna wasu yankunan jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya sun ce ƴan bindiga sun kai musu ƙazamin hari tare da garkuwa da mutane da dama a garin Shadaɗi.

Harin da aka kai a ranar Laraba na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke rincaɓewa a yankunan Neja tun bayan da gwamnan jihar ya tabbatar da cewa ƴan Boko Haram sun shiga garin.

Yanzu haka jama’ar garin Shadaɗi da ke karamar hukumar Mariga na cewa dubban mutane sun tsere bayan da ƴan bindigar suka kai masu hari.

Sannan akwai masu cewa waɗanda aka kashe sun haura mutum 100, adadin da gwamnatin jihar ta ce bai kai haka ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: