Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya sha alwashin cewa APC za ta karɓe dukkan kujerun ƴan Majalisar Tarayya na jihar a 2027 Umar Namadi ya bukaci sanatan PDP ɗaya da ƴan Majalisar Wakilai biyu su fara shirye-shiryen baro Majalisar Tarayya Ya ce yadda APC ke kara shiga lungu da saƙo ya nuna cewa jam’iyyar ba za ta bar kowace kujera ba a zaɓe na gaba.
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya shawarci ‘yan majalisar tarayya na jam’iyyar PDP su fara shirye-shiryen haɗa kayansu su dawo gida a 2027. Gwamna Umar Namadi wanda ake kira da Ɗanmodi ya sha alwashin cewa jam’iyyarsa ta APC za ta lashe duk wata kujera a jihar Jigawa a zaɓe mai zuwa.