Asirin wayanda suke kaiwa yan Boko Haram takin noma ya fara tonuwa

0 79

Rundunar Sojin Najeriya ta kama wani mutum mai suna Yusuf Saleh bisa zarginsa da kaiwa yan kungiyar Boko Haram da takin zamani.

Cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na rundunar Sojin Najeriya Onyema Nwachukwu, ya ce rundunar Operation Hadin Kai ce wanda take aikin a yankin ta kama mutumin a yankin Bayamari na karamar hukumar Geidam ta Jihar Yobe.

Nwachukwu, ya ce rundunar ta kama mutumin dauke da buhunan takin Zamani 38 masu nauyin 50kg, bayan sun binciki mutumin.

A cewarsa gwamnatin tarayya ta haramta amfani da takin zamani na Urea a yankin saboda mayakan suna amfani dashi wajen tashin bama-bamai.

Haka kuma ya ce a yanzu haka, mutumin yana cigaba da tallafawa rundunar da bayanan sirri wanda zai tallafa mata.

Kazalika, ya umarci mutane su cigaba da tallafawa sojojin da bayanan sirri ta yadda hakan zai taimakesu su gudanar da ayyukan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: