Atiku Abubakar ya yi alkawarin fitar da Najeriya daga cikin duhu matukar aka zabe shi a shugaban kasa

0 84

Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyar PDP a zaben shekarar 2023 Atiku Abubakar, ya yi Alkawarin fitar da Najeriya daga cikin Duhu matukar aka zabe shi a shugaban kasa.

Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da Daftarinsa kan yadda zai ciyar da tattalin Arzikin Kasa gaba, a taron Jin Ra’ayoyin Yan Takarar Shugaban Kasa kan Bunkasa Tattalin Arzikin Fannoni Masu Zaman Kansu, wanda Cibiyar Kasuwanci Da Masana’antu ta Shirya a Lagos.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, ya shawarci yan Najeriya da kada su bari taken Jam’iyu su kawar da su daga irin shirye-shiryen cigaban da ya tanadarwa Kasar.

Haka kuma ya bukaci Al’umma da suyi watsi da Karerayin da ake yadawa a shafukan Facebook da Twitter da Instagram, inda ya ce kafofin basa samar da Mafita ga matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da kuma Siyasa ga Kasa.

Da ya ke gabatar da kudurinsa, Atiku Abubakar, ya koka kan yadda tattalin arzikin kasar nan ya ke samun koma baya maimakon cigaba.

A cewarsa, bashika sun yiwa kasar nan yawa, abinda ya ke nuni da cewa dole ne a magance matsalar.

Kazalika, ya ce tun cikin shekarar 2015, Gwamnatin APC ta ke ciyo bashi domin aiwatar da kasafin kudin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: