A wani cigaban kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace dole a cigaba da amfani da na’urar BVAS a matsayin abin tantance masu kada kuri’a da aikawa da sakamakon zabe a Najeriya.
Atiku Abubakar, wanda shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben watan Fabrairun bana, ya fadi haka cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin yada labaransa a Abuja.
An fitar da sanarwar ne a matsayin martanin hukuncin kotun koli da ya tabbatar da Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a matsayin gwamnan jihar.
A wani labarin kuma, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun yayi alkawarin samarwa mutanen jihar karin romon demokradiyya bayan kotun koli ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.
Ademola Adeleke wanda ya zanta da ‘yan jarida a jiya a gidansa dake Ede, jim kadan bayan kotun koli ta tabbatar da sahihancin nasarar zabensa na gwamna da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yulin bana, yace aikin dake gabansa shine tabbatar da cewa mazauna jihar sun sharbi romon demokradiyya.